<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ya Allah, Mai Ƙauna LW325</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Allah, mai ƙauna,
 Zo, ka kusance mu,
 Ka duba amarya da angonta.
 Sun zo su yi wa juna alkawari.
 Ya Allah, sa albarka,
 Ka cika su da murna,
 Ka haɗa su da ƙauna mafificiya.

[V2]
 2) Alkawarin aure
 Abu ne mai tsarki,
 Kada su tsinke shi tun suna da rai
 Ko cikin daɗi ko a cikin ƙunci
 Ka sa su yi aminci,
 Ka riƙe su da ƙarfi,
 Ka ɗaura musu aure mai lafiya.

[V3]
 3) Ya Yesu, mai ƙauna,
 Ango na Ekklesiya,
 Kai ne masoyin dukan tsarkaka.
 Zauna tare da mijin da matarsa,
 Ka bi da su, ya Yesu,
 Ka zama Shugabansu,
 Ka mai da su, ya Yesu, masoyanka.</lyrics>
<hymn_number>325</hymn_number>
<author>Wade, John Francis (circa 1710-1786), Hillsong Worship</author>
</song>